
Gwamnatin jihar Neja ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantun firamare da sakandare na gwamnati da kuma masu zaman kansu dake faɗin jihar biyo bayan sace daliban makarantar St.Mary Catholic School dake Papiri a ƙaramar hukumar Agwara ta jihar
Gwamnan jihar Umar Bago ne ya sanar da umarnin a ranar Asabar bayan wani taro kan tsaro da yayi da shugabannin hukumomin tsaro
“Gwamna Umaru Bago shi ne ya fadi haka jim kaɗan bayan taro kan tsaro da ya yi shugabannin hukumomin tsaro biyo bayan garkuwar da aka yi da yara dalibai a makarantar St.Mary’s Catholic School dake Papiri a ƙaramar hukumar Agwara, ” a cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Balogi Ibrahim ya fitar.
“Manomin gwamna Bago ya ce dukkanin makarantun mishin, Islamiyya da kuma Makarantun Sakandaren gwamnatin Tarayya za su da ka ta da aiki har sai baba ta gani,”
“Har ila yau manyan makarantun gaba da sakandare dake mazabar majalisar dattawa ta arewacin Neja da kuma sauran yankunan da suke fuskantar barazana a shiyar gabashin jihar suma za a rufe su.”
Gwamnan ya yi kira ga jami’an tsaro ya yi kira jami’an tsaro, kungiyoyin farar hula, kungiyoyin kwadago da malaman addini kan su mayar da hankali wajen kokarin da ake na kubutar da daliban.

