
Biyu daga cikin dalibai mata 25 da yan bindiga su ka yi garkuwa da su daga makarantar sakandaren yan mata ta Maga dake jihar Kebbi sun tsere daga hannun waɗanda su ka yi garkuwa da su.
Hussaini Aliyu wani jami’in karamar hukumar Danko Wasagu ya fadawa BBC cewa daliban biyu sun tsere cikin gonaki lokacin da yan bindigar suka tasa keyarsu a cikin daji.
Kafar yada labarai ta BBC ta rawaito Aliyu na cewa yan matan sun dawo gida kalau sai daya daga cikinsu na bukatar kulawar likitoci saboda rauni da ta samu kafarta.
Da tsakar daren ranar Litinin ne yan bindigar suka kai farmaki makarantar inda suka sace dalibai 25 tare da kashe mataimakin shugaban makarantar da kuma wani maigadi.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Nafiu Kotarkoshi ya ce Hassan Makuku mataimakin shugaban makarantar ya rasa ransa a harin a yayin da Ali Shehu wanda maigadi ne ya samu rauni a hannunsa.
Amma rahoton na BBC ya bayyana cewa Shehu ya mutu a asibiti sakamakon raunin da ya samu.

