An samu tashin hankali a hedikwatar jam’iyyar PDP da ke Abuja bayan yunƙurin gudanar da taruka guda biyu daga sassa daban-daban na jam’iyyar.
Kwamitin NWC da aka zaba a Ibadan da kuma ɓangaren da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ke goyon baya sun shirya taronsu a rana ɗaya.
Sakataren jam’iyyar na ɓangaren Wike, Samuel Anyanwu, ya isa Wadata Plaza tare da wasu magoya baya. Bayan ɗan lokaci kuma, tawagar Taminu Turaki ta iso amma aka hana su shiga.
Duk da hakan, wasu gwamnoni biyu sun samu nasarar kutsa kai cikin ginin. Yayin da sauran mambobin ɓangaren suka yi ƙoƙarin shiga, jami’an tsaro suka bude wuta a sama tare da sakin hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa jama’a. Wannan ya jawo firgici, mutane suka fara gudu domin tsira da rayukansu.
Tun kafin rikicin, Anyanwu ya shaida wa manema labarai cewa karin tsaro al’ada ce domin kiyaye doka da oda. Ya ce ɓangarensu ya shirya taron BoT da na NEC.
An ji Karar Harbe-harbe A Sakatariyar PDP A Abuja

