Gwamnatin Jihar Kano ta sake gurfanar da Isma’il Dahiru Ajingi a gaban Babbar Kotun Jihar Kano da ke zaune a Sakatariyar Audu Bako, karkashin jagorancin Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu.
Ana tuhumarsa da laifin kisa, wanda ya saba da Sashe na 221 na Dokar Penal Code.
Lauyan gwamnati, Barista Lamido Abba Soran Dinki, ya gabatar da wani shaida a gaban kotu, wanda shi ne ASP Abdullahi Sajo, jami’in ‘yan sanda da ya jagoranci binciken lamarin.
Shaidan ya bada cikakken bayani game da yadda abin ya faru, daga baya kuma aka sallame shi daga gaban kotu.
Alkalin kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 27 ga Janairu, 2026 domin ci gaba da bincike.
Rahotanni sun nuna cewa wanda ake tuhuma ya kashe mahaifinsa ne ta hanyar caka masa wuka bayan sabani da suka samu a gonar albasa.
Rahoton ya ce rikicin ya samo asali ne bayan mahaifin ya ki amincewa da bukatar ɗan nasa ta ƙara aure.
Lamarin ya faru ne a ranar 22 ga Afrilu, 2024, a ƙauyen Unguwar Bai da ke cikin Ƙaramar Hukumar Ajingi a Jihar Kano.

