
Wata babbar kotu dake zamanta a Abuja ta dakatar da jam’iyar PDP daga gudanar da babban taronta da aka shirya yi a Ibadan babban birnin jihar Oyo a tsakanin ranakun 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba.
Har ila yau kotun ta hana hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC sanya ido, lura ko kuma amincewa da duk wani mataki da aka dauka a wurin taron matukar aka gudanar da shi.
Alkalin kotun mai shari’a, Peter Lifu shi ne ya bayar da umarnin a ranar Talata lokacin da yake yanke hukunci kan karar da Sule Lamido tsohon gwamnan jihar Jigawa ya shigar gaban kotun.
Lamido ya kai karar jam’iyar ne kan zargin hana shi damar sayen fom din tsayawa takarar shugabancin jam’iyar domin ya samu damar shiga babban taron na zaben shugabannin.
A ranar 31 ga watan Oktoba ne Lamido ya shigar da kara gaban kotun inda yake bukatar umarnin gaggawa ta dakatar da babban taron zaben shugabannin jam’iyar.
Alkalin kotun ya umarci wanda ake kara na farko da na biyu wato PDP da INEC da da su bada dalilin da zai gamsar da kotu kada ta amince da bukatar da mai kara yake bukata a gabanta.
A yayin da aka dawo zaman kotun na ranar Talata mai shari’a Lifu ya gamsu cewa lallai bukatar da mai kara ya gabatar gaban kotun abun dubawa ce dake bukatar sauraren kotun.

