Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da rage kuɗin da masu niyyar zuwa aikin Hajji za su biya a shekarar 2026, inda ta ce sabon farashin ya yi ƙasa idan aka kwatanta da na bara.
Bisa bayanan da hukumar ta fitar, masu niyyar zuwa Hajji daga yankin Borno da Adamawa za su biya naira 7,579,020.96 maimakon naira 8,327,125.59 da aka biya a 2025.
Haka kuma, daga yankin Arewa za a biya naira 7,696,769.76, yayin da daga Kudanci za a biya naira 7,991,141.76 — duka da raguwar kaso mai yawa a kan na bara.
NAHCON ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X (Twitter) a ranar Litinin, inda ta ce matakin na nufin sauƙaƙa wa Musulman Najeriya damar zuwa aikin Hajji a shekara mai zuwa.
Hukumar ta kuma bayyana ranar 5 ga Disamba, 2025 a matsayin ƙarshe ga masu niyyar zuwa Hajji su kammala biyan kuɗinsu.
A baya dai, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci NAHCON ta sake duba kuɗin Hajjin domin rage nauyi a kan alhazai.
NAHCON Ta Rage Kuɗin Hajjin 2026, Ta Sa Ranar Ƙarshe Ta Biyan Kuɗi

