Ban Zargi Kashim Shettima Da Kafa Kungiyar B.H. Ba—Ali Modu Sheriff

Tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya karyata rahotannin da ake yadawa a kafafen sada zumunta da ke cewa ya zargi Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da kafa ƙungiyar Boko Haram.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar Sanata Sheriff ya bayyana labarin a matsayin ƙarya marar tushe, mai nufin haifar da rikici da rarrabuwar kawuna.

A cewarsa, “An jawo hankalin tsohon Gwamnan Jihar Borno kuma dattijo mai mutunci, Sanata Ali Modu Sheriff, kan wani labari na ƙarya da ke yawo a yanar gizo mai taken ‘Ba Ni Ba ne, Shettima Ne Ya Ƙirƙiri Boko Haram — In Ji Sheriff.’”

Ya ce labarin duk ƙirƙira ne wanda babu gaskiya cikinsa, kuma an yi shi da gangan domin ya yaudari jama’a tare da bata masa suna.

Sheriff ya bayyana cewa bai taɓa yin irin wannan magana ba, ko yin wata hira kan batun ba, balle ma yin wata tattaunawa da ‘yan jarida. Ya ƙara da cewa wannan rahoto na bogi na iya zama barazana ga zaman lafiya da ci gaban ƙasa.

Ya bukaci jama’a da kafafen yada labarai su yi watsi da labarin, yana mai gargadin cewa lauyoyinsa sun fara aiki domin gano masu yaɗa labarin tare da ɗaukar matakin doka a kansu.

Sheriff ya kuma yi barazanar kai ƙarar wadanda suka yaɗa wannan labari idan ba su janye ba, yana jaddada aniyarsa ta kare gaskiya, adalci, da mutuncinsa a matsayin ɗan siyasa da dattijo mai kishin ƙasa.

More from this stream

Recomended