Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Alhaji Muhammad Sama’ila-Bagudo, ya kuɓuta daga hannun ‘yan bindiga bayan kwana da dama da aka yi da shi a cikin daji.
Rahotanni sun nuna cewa an sace Sama’ila-Bagudo ne a garinsa na Bagudo, da ke Ƙaramar Hukumar Bagudo ta jihar, a ranar Juma’a, 1 ga watan Nuwamba, bayan ya idar da sallar magariba kuma yake kan hanyarsa ta komawa gida daga masallaci.
Wani gidan rediyo a Birnin Kebbi ta tabbatar da sakin ɗan majalisar, sai dai ba ta bayar da cikakken bayani kan yadda aka sake shi ba a lokacin da ake gabatar da rahoton.
Da ƴan jarida suka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Nafiu Abubakar, ya ce yana buƙatar ƙarin lokaci domin tabbatar da labarin.
Sai dai daga baya, mai magana da yawun jam’iyyar APC ta jihar Kebbi, Isa Assalafy, ya tabbatar da cewa an sake Mataimakin Kakakin Majalisar a ranar Asabar, yana mai cewa jami’an tsaro za su fitar da ƙarin bayani daga bisani.
An dai sace Sama’ila-Bagudo ne a wani lokaci da matsalar tsaro ke ci gaba da addabar yankunan karkara na jihar Kebbi, musamman ta hanyar hare-haren ‘yan bindiga da sace-sacen mutane domin neman kuɗin fansa.
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Ya Kuɓuta Daga Hannun ‘Yan Bindiga

