Tinubu Ya Ce Gwamnatin Najeriya Ba Za Ta Bari A Tsoratar Da Ita Ba



Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Najeriya ba za ta bari kowace ƙasa ta tsoratar da ita ba, duk da damuwar da ake nunawa a duniya game da zargin kisan gillar da ake yi wa Kiristoci a ƙasar.

Tinubu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X (tsohon Twitter) a ranar Juma’a, kwanaki bayan shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar kai farmakin soja a Najeriya bisa zargin cewa ana kashe Kiristoci a ƙasar.

Shugaban ƙasa ya ce Najeriya za ta ci gaba da taka rawarta a idon duniya cikin natsuwa da fahimta da kuma cikakken tsari na gaskiya.

Game da matsalar tsaro, Tinubu ya bayyana cewa taɓarɓarewar tsaro da ta samo asali daga ta’addanci na ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta tsawon shekaru, amma gwamnatin sa tana da cikakken niyyar kawo ƙarshen lamarin.

A cewarsa: “Lallai muna fuskantar matsalar ta’addanci — ƙalubale ne da Najeriya ta jima tana fama da shi, amma ba za mu ja da baya ba. Za mu yi nasara a wannan yaki. Tsaro abu ne da ba za a yi wasa da shi ba, kuma ba za mu taɓa yin sulhu da wannan manufa ba. Da ƙarfin guiwa da bin doka, za mu yi nasara.”

Tinubu ya jaddada cewa tsaron ƙasa ba abin tattaunawa ba ne, yana mai tabbatar da cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kawar da duk wata barazana ga zaman lafiya.

Haka kuma, ya yi kira ga ƙasashen duniya su ci gaba da ba Najeriya goyon baya, yana mai cewa haɗin kai tsakanin ƙasashe na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da ci gaban da aka riga aka samu.

Wannan jawabi na Tinubu na zuwa ne bayan barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi, inda ya bayyana cewa ya umurci Ma’aikatar Tsaron Amurka da ta shirya yiwuwar kai farmaki a Najeriya idan gwamnatin ƙasar ta ci gaba da “lamunce wa kisan Kiristoci.”

Trump ya kuma sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargin suna da matsalolin cin zarafin Kiristoci, a matsayin ƙasa mai “damuwa ta musamman.”

More from this stream

Recomended