Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Borgu da Agwara, Jafaru Mohammad Ali Damisa, ya tsira daga harin da ake zargin ’yan ta’adda ne suka kai masa a yankin Lumma–Babanna da ke karamar hukumar Borgu, Jihar Neja.
Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne a ranar Talata yayin da Damisa ke kan hanyarsa zuwa Babanna domin wani aiki na ofis.
Wata majiyar tsaro ta ce maharan, da ake kira “Lakurawa” a yankin, sun bude wuta a kan ayarin dan majalisar.
Jami’an tsaro da ke rakiyar sa sun mayar da martani, sai dai wani soja ya rasa ransa a fafatawar, yayin da wasu suka ji rauni kuma aka garzaya da su asibiti.
Shaidu sun ce maharan sun yi ta harbi ba kakkautawa, inda suka lalata motoci kusan goma sha ɗaya kafin daga baya jami’an tsaro su kwashe su daga wurin.
Duk da tsanantar harbin bindiga, Damisa bai ji rauni ba.
Dan Majalisa Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Wani Harin ‘Yan Bindiga A Jihar Neja

