
Hukumar NRC dake lura da zirga-zirgar jiragen kasa a Najeriya ta dakatar da zirga-zirgar jirgin kasa daga Warri zuwa Itakpe bayan da jirgin ya kauce daga kan digarsa a ranar Asabar.
A wata sanarwa da aka fitar ranarĀ Lahadi, shugaban hukumar kuma babban jami’in gudanarwarta, Kayode Opeifa ya ce lamarin ya faru ne da misalin Ęarfe 07:30 na daren ranar Asabar a daid kilomita 212 da mita 8 a garin Agbor.
Opeifa ya ce an samu nasarar kwashe dukkanin fasinjojin dake cikin jirginĀ ba tare da samun wanda ya jikkata ba ko kuma ya mutu.
Ya kara da cewa binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa batagari suna ka lalata titin jirgin ta hanyar sace karafa abun da ya yi sanadiyar hatsarin da ya shafi tarago biyu na jirgin kasar.
Hatsarin jirgin na zuwa ne kasa da mako biyu da hukumar ta sanar da dawo da zirga-zirgar jirgin kasa a tsakanin garin Warri dake jihar Delta da kuma Itakpe a jihar Kogi biyo bayan kammala gyaran layin dogon da wasu bata gari suka lalata.

