Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas ta sake cafke wani tsohon fursuna mai shekara 25 da haihuwa, tare da wasu mutum biyu da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a sassan jihar.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abimbola Adebisi, ta tabbatar da kama mutanen cikin wata sanarwa da ta fitar ga manema labarai a Legas ranar Alhamis.
Ta bayyana cewa jami’an sashen Rapid Response Squad (RRS) ne suka kama tsohon fursunan, wanda aka sako daga Kurkukun Kirikiri kwanaki biyar kacal da suka gabata.
Adebisi ta ce, “An kama wanda ake zargi da safiyar Talata da misalin ƙarfe 8:00 na safe a kasuwar Oshodi, bayan an lura da motsinsa da ba na al’ada ba.
“An same shi da Naira 80,000 da wayar Infinix Note 40 Pro, waɗanda aka gano cewa ya sata ne a wani gidan kasuwa da ke Opebi, inda ya sace Naira 200,000 da wayar daga hannun wani ɗan kasuwa da yake barci.
“An kuma samo tufafi da takalma da ya saya daga cikin kudin da ya sace,” in ji ta.
A wani samame dabam, mai magana da yawun ta bayyana cewa jami’an RRS sun kuma kama wasu masu fashin aljihu biyu masu shekaru 21 da 27, bayan sun yi ƙoƙarin satar wayoyi daga hannun fasinjoji a wurare daban-daban na Legas.
Mai magana da yawun ta kuma ce kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Mista Olohundare Jimoh, ya yaba da ƙwarewa da himmar jami’an RRS wajen gudanar da aikin.
‘Yan Sanda Sun Kama Tsohon Fursuna Da Ya Koma Fashi Kwanaki Biyar Bayan Fitarsa Daga Kurkuku

