An sako Sowore daga gidan yarin Kuje bayan cika sharudan beli

Omoyole Sowore dan gwagwarmaya kuma mai fafutukar kare hakkin bil’adama ya fito daga gidan yarin Kuje bayan da ya cika sharudan beli da kotu ta gindaya masa.

An sako Sowore a ranar Litinin tare da Aloy Ejimakor  tsohon lauyan Nnamdi Kanu da kuma wasu mutane 11 da suka shiga zanga-zangar neman sakin Nnamdi daga hannun jami’an tsaro.

Tun shekarar 2021 ne Nnamdi Kanu ya ke tsare a hannun jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS tun bayan da suka kama shi.

A ranar Juma’a ne yan sanda  suka gurfanar da wasu mutane 11 tare da Sowore da Ejimakor a gaban kotu inda ake tuhumarsu da tayar da hankalin jama’a bayan da suka shiga zanga-zangar da aka kira FreeNnamdiKanu wacce aka gudanar a birnin tarayya Abuja .

Alkalin Wata kotun majistire dake Abuja ne ya bayar da belin mutanen bisa sharadin  cewa kowannensu zai kawo mutum biyu da za su tsaya masa kan kudi naira ₦500,000,

Har ila dole mutanen su gabatar da nambarsu ta NIN, shedar biyan haraji da kuma fasfonsu na tafiye-tafiye.

More from this stream

Recomended