2027: Aregbesola Ya Bayyana Dalilan Da Zasu Sa Tinubu Ya Fadi Zabe

Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida kuma Sakataren Janar na Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Rauf Aregbesola, ya bayyana dalilan da suka sa yake ganin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai fadi zaben shekarar 2027.

Aregbesola ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a birnin Ilorin, yayin da yake magana da manema labarai bayan kaddamar da sabon ofishin jam’iyyar ADC na jihar Kwara da ke Basin Road.

Ya ce duk da yadda jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ke nuna karfinta, jam’iyyar ADC ce za ta karbi madafun iko a Najeriya da wasu jihohi.

A cewarsa, “Da gaske ne APC tana da karfi, da ba za ta yi ta damuwa da farautar ‘yan adawa a ko’ina cikin kasar nan ba. Amma abin da suke yi yanzu, na nuna cewa suna tsoratar da mambobinmu da shugabanninmu daga Lagos har zuwa Kebbi da Kaduna.”

Aregbesola ya kara da cewa, “Idan sun yi imani da karfinsu, za su kasance cikin natsuwa. Amma akasin haka ne abin yake, wanda hakan ke nuna cewa sun san basu da farin jini a wajen jama’a. Jam’iyyar ADC ce za ta amfana da rashin farin jininsu.”

Ya ce, “Ko da yake suna nuna isa, amma da ikon Allah ADC za ta karbi mulkin kasar nan da yawancin jihohi.”

Da yake tsokaci kan wasu gwamnonin da suke komawa jam’iyyar APC, tsohon ministan ya bayyana cewa “wadanda suke komawa APC makiyan jama’a ne.”

Haka kuma, tsohon gwamnan jihar Kwara, Alhaji Abdulfatah Ahmed, wanda ya bar jam’iyyar PDP ya koma ADC, ya shaida wa manema labarai cewa jam’iyyarsu ta shirya tsaf domin karbar mulki a kasa baki daya.

More from this stream

Recomended