
Shugabannin kananan hukumomi shida sun bayyana goyon bayansu ga gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri kan sauya shekar da ya yi zuwa jam’iyar APC daga PDP.
A ranar Laraba gwamnan ya sanar da ficewarsa daga jam’iyar adawa ta PDP saboda wasu dalilai da ya ce bayyanannu a fili.
Diri ya kara da cewa mambobin majalisar zartarwa ta jihar da kuma yan majalisar dokoki ta jihar sun fice daga jam’iyar ta PDP a tare da shi.
Biyo bayan haka ne su ma shugabannin Æ™ananan hukumomi Æ™arÆ™ashin kungiyar ALGON suka sanar da fitarsu daga jam’iyar PDP a wani taron manema labarai da suka yi a ginin sakatariyar kungiyar dake birnin Y
Lelei Tariye Isaac, shugaban karamar hukumar Kolokuma/Opokuma wanda ya yi magana a matsayin shugabannin kananan hukumomin ya ce sun dauki matakin saboda rikicin da ya dabaibaye jam’iyar ta PDP.