Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ondo ta kama wani tsohon fursuna mai shekaru 37 da ake zargi da kashe masoyiyarsa bayan rikici ya barke tsakaninsu kan bashin Naira 100,000 da ta ba shi.
Wanda ake zargin mai suna Ademola Omokinwa, ya lakada wa budurwarsa mai suna Joy Jimoh duka har ta mutu bayan ta nemi ya biya mata kuɗin da ta ba shi aro.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Olayinka Ayanlade, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa abin ya faru ne a garin Idanre.
A cewarsa, wata maƙwabciyar mamaciyar mai suna Ngozi Gregory ce ta kai rahoton lamarin ofishin ‘yan sanda, inda nan da nan jami’an tsaro suka tafi wajen domin kama wanda ake zargin.
Ayanlade ya bayyana cewa, “Rahoton ya nuna cewa yayin cacar baki tsakaninsu, wanda ake zargin ya fusata ya kuma yi ta bugun budurwarsa har ta suma.
“An garzaya da ita asibiti domin kulawar gaggawa, sai dai likita ya tabbatar da cewa ta mutu. Daga nan aka kai gawarta dakin ajiye gawa domin binciken likitanci. Haka kuma an fara bincike a ofishin ‘yan sanda.”
Ya ƙara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar da umarnin a mika ƙarar ga sashen binciken manyan laifuka na jihar (State CID) domin gudanar da cikakken bincike cikin kwarewa da gaskiya.
Rundunar ta bayyana cewa za ta tabbatar da ganin an hukunta wanda ake zargi daidai da doka, tare da jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar Ondo.
Wani Tsohon Fursuna Ya Hallaka Budurwarsa Saboda Bashin Naira 100,000
