Sojoji Sun Ceto Mutane Tara Da ‘Yan Bindiga Suka Sace a Kwara

Sojojin Rundunar 22 Armoured Brigade ta rundunar sojin Najeriya da ke Sobi a jihar Kwara sun ceto mutane tara da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin Matokun da ke cikin karamar hukumar Patigi ta jihar.

Wata majiya ta tsaro ta tabbatar da cewa an mika waɗanda aka ceto ga shugaban karamar hukumar Patigi, wanda kakakin majalisar yankin, Mohammed Usman Alhaji, ya wakilta.

Bayan haka, an garzaya da mutanen da aka ceto zuwa wani asibiti da ba a bayyana ba domin a duba lafiyarsu tare da ba su kulawar da ta dace.

Rundunar 22 Armoured Brigade ta sake jaddada kudirinta na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar Kwara. Rundunar ta kuma yi alkawarin ci gaba da aikin ceto sauran mutanen da ke hannun masu garkuwa da su har sai an dawo da cikakken zaman lafiya a jihar da ake kira State of Harmony.

Da yake magana a madadin al’ummar Patigi, Mohammed Gana Alhaji ya nuna godiya ta musamman ga sojojin rundunar bisa jajircewar da suke nunawa wajen yakar matsalar rashin tsaro da kare al’ummomin yankin daga hare-haren ‘yan ta’adda.

Jaridu sun ruwaito cewa a ranar 23 ga Satumba, 2025, ‘yan bindiga sun kai mummunan hari a wasu kauyuka da ke cikin karamar hukumar Patigi, inda suka kashe wata mata mai juna biyu a kauyen Matokun, suka jikkata wasu, sannan suka sace mutane takwas.

More from this stream

Recomended