Majalisar Wakilan Tarayya ta bukaci Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) da su koma teburin tattaunawa cikin gaggawa domin warware matsalolin da suka janyo sanarwar fara yajin aikin gargadi na makonni biyu da ƙungiyar ta ayyana.
Wannan umarni na majalisar ya biyo bayan amincewa da kudurin gaggawa da ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Badagry ta Jihar Legas, Mista Oluwaseun Whinghan, ya gabatar yayin zaman majalisar a ranar Talata.
Rahotanni sun nuna cewa ASUU ta fara yajin aikin gargadi a ranar Litinin bisa zargin gwamnatin tarayya ta gaza magance wasu matsaloli da suka daɗe suna jawo takaddama tsakaninta da ƙungiyar.
Ƙungiyar ta bayyana cewa cikin manyan batutuwan da suke ƙalubalantar gwamnati akwai aiwatar da yarjejeniyar ASUU da gwamnatin tarayya ta shekarar 2009, batun kuɗin farfaɗo da jami’o’i, alawus ɗin malamai, tsarin albashi, da kuma ikon gudanar da harkokin jami’a ba tare da tsoma bakin gwamnati ba.
Kafin ASUU ta soma yajin aikin, Ministan Ilimi, Dakta Yusuf Sununu, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na kammala matakan tattaunawa da ƙungiyar domin kawo ƙarshen dukkan batutuwan da ke kawo sabani.
Yayin gabatar da kudurinsa, Whinghan ya nuna damuwa matuƙa kan sabuwar takaddamar, yana mai gargadin cewa irin wannan yajin aiki a baya kan rikide zuwa na dogon lokaci wanda ke lalata tsarin karatu, rushe bincike, da kuma jefa ɗalibai, iyaye da malamai cikin damuwa.
Ya ce, “Majalisar ta lura cewa ko da ASUU ta bayyana wannan yajin aiki a matsayin na gargadi, abubuwan da suka gabata sun nuna cewa irin waɗannan matakai kan rikide zuwa dakatar da aiki na tsawon lokaci.
“Muna sane da cewa tsarin jami’o’in Najeriya na da muhimmanci ga ci gaban ƙasa, kirkire-kirkire, da bunƙasar ɗan adam. Duk wani tsaiko a cikinsa na raunana gasa ta ƙasa, cigaban kimiyya, da kuma aikin matasa,” in ji shi.
Whinghan ya ƙara da cewa, bisa kundin tsarin mulkin ƙasar na shekarar 1999 (sashi na 18), ilimi na daga cikin ginshiƙan cigaban jama’a da fasaha, don haka ya zama wajibi a kan gwamnati da ƙungiyoyin jami’o’i su haɗa kai wajen tabbatar da dorewar ingancin sa.
Majalisar ta jaddada bukatar a hanzarta warware rikicin domin kada ya sake jefa tsarin karatu a cikin rudani kamar yadda aka saba gani a baya.
Majalisar Wakilai Ta Nemi Gwamnatin Tarayya Da ASUU Su Tattauna Don Magance Yajin Aikin Malaman Jami’a
