Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta sanar da fara yajin aiki na tsawon mako biyu, wanda zai kasance cikakke kuma gargaɗi, a dukkan jami’o’in gwamnatin tarayya da na jihohi a fadin Najeriya.
Shugaban kungiyar, Farfesa Chris Piwuna, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a ranar Lahadi, 12 ga Oktoba, 2025, a Jami’ar Abuja.
“Saboda haka, dukkan rassan ASUU ana umartar su da su janye duk ayyukan koyarwa da bincike daga misalin karfe 12 na dare na Litinin, 13 ga Oktoba, 2025.
“Yajin aikin zai kasance cikakke ne da kuma gargaɗi, kamar yadda aka amince a taron NEC na ƙarshe,” in ji shi.
Rahotanni sun nuna cewa wannan sabuwar takaddama tsakanin malaman jami’a da gwamnatin tarayya ta taso ne duk da ci gaba da tattaunawa da ake yi domin guje wa sake samun rikici a jami’o’in kasar.
A ranar Laraba, Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya bayyana a Abuja cewa gwamnati ta shiga matakin ƙarshe na tattaunawa da ASUU da sauran ƙungiyoyi domin warware matsalolin da suka shafi albashi, walwala, da aiwatar da yarjejeniyar ASUU-FGN ta 2009.
Alausa ya kara da cewa gwamnatin Tinubu ta riga ta saki naira biliyan 50 domin biyan kuɗaɗen ƙarin aikin malamai (Earned Academic Allowances), yayin da aka kuma ware biliyan 150 a cikin kasafin kuɗin 2025 don bukatun gyaran jami’o’i, wanda za a rarraba a matakai uku.
Ana sa ran karin bayani zai biyo baya daga ofishin ASUU a kwanaki masu zuwa.
ASUU Ta Ayyana Yajin Aiki Na Tsawon Mako Biyu A Fadin Jami’o’in Gwamnati
