Wata motar tifa ta markade mai babur

Wata motar tifar  yashi dake tsaka da da tsala gudu ta bi ta kan wani mai babur inda ta markade shi har lahira akan titin Oda dake Akure babban birnin jihar Ondo.

Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Laraba kuma matukin babur din ya mutu nan take.

Wani shedar gani da ido ya ce motar ta kwace ne inda ta bi ta kan mai babur din.

“Lamarin ya faru kamar kiftawar ido inda ya jefa mazauna wurin da ma masu wuce a cikin jimami,” ya ce.

Marigayin wanda kawo yanzu ba a gano sunansa ba  an ce yana kan hanyarsa ta komawa gida ne bayan da ya sauke dansa a makaranta.

Matukin motar yashin ya tsere a kafa  biyo bayan faruwar lamarin.

More from this stream

Recomended