‘Yan Sanda Sun Hallaka ’Yan Bindiga Uku A Karamar Hukumar Dandi Ta Jihar Kebbi

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi ta tabbatar da cewa jami’anta tare da taimakon ‘yan sa kai sun kashe wasu ‘yan bindiga uku da ake zargin Lakurawa ne a wani samame da aka kai a ƙauyen Gorun Yamma, cikin ƙaramar hukumar Dandi.

Mai magana da yawun rundunar, CSP Nafiu Abubakar, ya bayyana cewa DPO na Kamba, Muhammed Bello, ne ya jagoranci samamen bayan samun sahihan bayanan sirri. Ya ce jami’an tsaro sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar na tsawon sa’o’i kafin a samu nasarar halaka wasu daga cikinsu.

A cewarsa, an gano mota ba tare da rajista ba daga wurin ‘yan bindigar, yayin da sauran suka tsere cikin daji da raunukan harbi, kuma sun barin makamai a bayan.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Bello M. Sani, ya yaba wa jami’an rundunar bisa jajircewarsu da kwazo a wajen yaƙi da miyagu. Ya kuma bukace su da su ci gaba da matsa kaimi kan duk wasu masu aikata laifi.

Sani ya tabbatar wa mazauna jihar cewa rundunar ‘yan sanda za ta ci gaba da aiki tukuru don tabbatar da cewa jihar Kebbi ta zama wuri da ba za a iya yin ta’addanci ko barna ba.

More from this stream

Recomended