Gwamna Uba Sani Ya Saki Naira Biliyan 2.3 Don Biyan Tsofaffin Ma’aikata Da Iyalan Ma’aikatan Da Suka Rasu

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya amince da sakin naira biliyan 2.321 domin biyan hakkokin fansho, gratuti da kuma kudaden ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya da iyalan wadanda suka rasu a fadin jihar.

Wannan biyan ya kunshi Accrued Rights karkashin tsarin Contributory Pension Scheme (CPS) da kuma Gratuity/Death Benefits karkashin tsohon tsarin Defined Benefit Scheme (DBS).

Da wannan kudin da aka saki, gwamnatin jihar Kaduna ta kai adadin N6.678 biliyan da aka biya a shekarar 2025 kadai, yayin da jimillar da aka biya tun bayan hawan gwamnatin yanzu ta kai biliyan N13.5 cikin shekaru biyu.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Ahmed Maiyaki, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa kula da walwalar tsofaffin ma’aikata na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin jihar ta dauka da muhimmanci. Ya ce gwamnati za ta ci gaba da tabbatar da biyan hakkokin fansho da sauran hakkoki cikin lokaci domin rage wahalhalun da tsofaffin ma’aikata ke fuskanta.

Shi ma Sakataren Hukumar Fansho ta Jihar Kaduna, Ibrahim Balarabe, ya bayyana cewa wannan sabon rukunin biyan zai amfanar da mutane 661, wanda suka hada da tsofaffin ma’aikata da iyalan wadanda suka rasu a matakin jiha da kananan hukumomi.

More from this stream

Recomended