‘Yan Bindiga Sun Kai Hari a Filato, Sun Halaka Mutum Daya, Sun Jikkata Wasu da Dama

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai sabon hari a jihar Filato, inda suka kashe wani mutum mai shekaru 65 da haihuwa tare da jikkata mutane da dama.

Shugaban ƙungiyar Berom Youth Moulders Association (BYM) na ƙasa, Barista Dalyop Solomon Mwantiri, ne ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin Asabar.

Ya ce maharan dauke da makamai sun afkawa kauyen Gako da ke yankin Rim, a ƙaramar hukumar Riyom, da daren Juma’a, 3 ga Oktoba, 2025, inda suka fara harbe-harbe ba tare da tsoro ba.

A cewarsa, an kashe mutum ɗaya mai suna Mista Bulus Dongo, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.

A cikin sanarwar, Mwantiri ya ce, “Yayin da ‘yan Najeriya ke jiran isowar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ziyarar ta’aziyya zuwa jihar Filato, wasu ‘yan ta’adda da ake zargin Fulani ne sun kai hari a kauyen Gako na yankin Rim da misalin ƙarfe 8:30 na dare, inda suka kashe Mista Bulus Dongo kuma suka jikkata wasu.”

Ya bayyana damuwarsa kan yadda harin ya faru duk da cewa an riga an fitar da gargaɗin cewa za a iya kai hari a yankin. “An tura sakon gargaɗi ga al’ummar yankin su kasance cikin shiri saboda yiwuwar hari, kuma abin takaici sai ga shi ‘yan bindigar sun kai farmaki,” in ji shi.

Mwantiri ya ƙara da cewa, bisa bayanan da ya samu daga mazauna yankin, maharan sun shigo kauyen ta gonakin masara da ke kewaye da wurin, inda suka harbe mutumin wanda ya mutu a wurin, inda ya bar matarsa da ‘ya’ya shida.

Ya kuma ce irin wannan mummunan lamari yakan faru ne bayan rikice-rikicen da ke tasowa saboda kiwon dabbobi a gonaki da kuma lalata amfanin gona da ke yawaita a yankunan Rim, Tahoss, Jol, Kwi, Wereng, Rahoss, Kogo da wasu ƙauyuka na makwabtaka.

More from this stream

Recomended