Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana cewa an yi wa kalamansa kuskuren fassara game da rawar da tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari ya taka a rikicin Boko Haram.
Jonathan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ikechukwu Eze, ya fitar a ranar Asabar.
A baya, yayin bikin ƙaddamar da littafin tsohon shugaban hafsan tsaron ƙasa, Lucky Irabor, a birnin Abuja, Jonathan ya ce ƙungiyar Boko Haram ta taɓa zaɓar Buhari a matsayin mai shiga tsakaninta da gwamnati a lokacin mulkinsa. Wannan maganar ta jawo cece-kuce musamman daga jam’iyyar APC mai mulki.
Sai dai a cikin sanarwar, Jonathan ta bakin mai magana da yawunsa ya ce, “an yi wa kalaman tsohon shugaban ƙasa mummunan fassara. A kowane lokaci, Dr. Jonathan bai taɓa nuna ko cewa Buhari yana da alaƙa da Boko Haram ba, ko kuma yana goyon bayan ƙungiyar a kowace hanya.”
Sanarwar ta bayyana cewa kalaman Jonathan a wajen taron, “sun yi nufin haskaka dabarun yaudara da ɓoyayyun hanyoyin da Boko Haram ke amfani da su a farkon shekarun ta.”
Tsohon shugaban ƙasar ya bukaci jama’a su yi watsi da duk wata fassarar da ba ta dace ba, yana mai jaddada cewa yana nan daram wajen neman zaman lafiya, haɗin kai, da kuma ƙarfafa ginshiƙan dimokuraɗiyya a Najeriya.
Jonathan Ya Musanta Danganta Buhari da Boko Haram
