Rahotanni sun bayyana cewa an gano gawar wani yaro mai shekaru 15 da haihuwa, Sunusi Abubakar, a wani tafki da ake kira Mahayin gidan Toro da ke kauyen Gabari, ƙaramar hukumar Dutse a jihar Jigawa.
Mahaifin mamacin, Abubakar Musa Gabari, ya shaida cewa lamarin ya faru ne bayan ɗansa ya tafi yin wanka a tafkin da misalin ƙarfe 5 na yamma amma bai dawo gida ba. Ya ce bayan ɓata lokaci, al’umma tare da jami’an tsaro suka shiga bincike, daga bisani kuma aka gano gawar yaron.
Mai magana da yawun hukumar NSCDC ta jihar Jigawa, ASC Badruddeen Tijjani Mahmud, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar. A cewarsa:
“Da misalin ƙarfe 9:00 na safe a yau Laraba 1 ga watan Oktoba 2025, rundunar NSCDC ta jihar Jigawa ta tabbatar da rasuwar wani yaro mai suna Sunusi Abubakar, ɗan kauyen Gabari a yankin Chamo, wanda aka gano gawarsa a cikin wani tafki da ake kira Mahayin gidan Toro, wanda ke da nisan kusan kilomita 1.5 arewa da kauyen Gabari.”
Ya ƙara da cewa kafin a gano gawar, an samu takalmi da wandon mamacin a bakin tafkin tun ranar 30 ga Satumba 2025.
ASC Badruddeen ya bayyana cewa babu wata alamar rauni a jikin yaron, inda daga bisani aka mika gawarsa ga iyayensa don gudanar da jana’iza bisa tsarin addinin Musulunci.
Hukumar NSCDC ta yi kira ga iyaye, masu kula da yara, da shugabannin al’umma da su rika gargadin yara da matasa kan yin wanka a ruwan da bai da tsaro domin kaucewa irin wannan mummunan lamari a nan gaba.
An Tsinci Gawar Wani Yaro Matashi A Cikin Tafki A Jihar Jigawa
