Gwamnatin tarayya ta sanar da sokewar faretin da aka shirya don bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai a ranar Laraba, 1 ga Oktoba.
A cikin wata sanarwa daga Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya wadda Daraktan Yaɗa Labarai, Segun Imohiosen ya sanya hannu, gwamnati ta bayyana hakan.
Sanarwar ta ƙara da cewa sauran shirye-shiryen bikin za su ci gaba kamar yadda aka tsara, ciki har da jawabai na shugaban ƙasa, al’adu, da kuma gasar National Campus Debate.
Da yake jawabi a taron manema labarai a Abuja, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya bayyana muhimmancin wannan rana.
Shi ma Ministan Yaɗa Labarai da Tsarin Ƙasa, Mohammed Idris, ya bayyana bikin na bana a matsayin mai muhimmanci. Ya kwatanta shekarun 65 da duwatsun sapphire da ke nuni da aminci, gaskiya da hikima.
Najeriya ta samu ‘yancin kai daga Burtaniya a ranar 1 ga Oktoba, 1960, kuma ana yawan yin bukukuwan tunawa da hakan ta hanyar paradin soja, addu’o’i da jawabai na shugabanni.
Cikar Najeriya Shekara 65 Da Ƴanci: Gwamnatin Tarayya Ta Soke Faretin Bikin Ranar ‘Yancin Kai
