Kungiyar kwadago ta TUC ta bayyana cewa za ta shiga yajin aikin kasa tare da PENGASSAN kan zargin danniyar ma’aikata da Kamfanin Dangote Refinery ke yi.
Sakataren TUC, Nuhu Toro, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.
Kungiyar ta bukaci a dawo da ma’aikatan da aka kora fiye da 800 saboda shiga PENGASSAN tare da neman kamfanin ya bada uzuri a bainar jama’a.
A cikin sanarwar, TUC ta ce: “Kongires ta umarci dukkan kungiyoyin da ke karkashinta su kasance cikin shirin shiga yajin aikin kasa idan kamfanin Dangote bai amsa wadannan bukatu cikin lokaci ba.
“Mun tsaya sosai wajen mara wa ma’aikatan da abin ya shafa baya da kuma kungiyar su PENGASSAN. An zalunce su ne kawai saboda sun bayyana cewa sun shiga kungiyar. Wannan kuwa hari ne kai tsaye ga Sashe na 40 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da kuma kan wajibcin da Najeriya ta dauka a yarjejeniyoyin ILO.
“Ba za mu bari kowanne kamfani, ko da kuwa yana da arziki ko girma ba, ya tauye mutunci da hakkokin ma’aikatan Najeriya ba. TUC ta tsaya daram kuma a shirye take ta dauki mataki mai karfi wajen kare ‘ya’yanta da ma’aikatan kasar nan.”
A karshen mako, PENGASSAN ta ayyana yajin aiki na kasa, inda ta umurci mambobinta su dakatar da isar da gas da man danyen mai zuwa Dangote Refinery.
Sai dai kamfanin ya bayyana matakin a matsayin “satar tattalin arziki.”
Hukumar NUPRC ta bukaci bangarorin biyu da su zauna teburin tattaunawa domin shawo kan rikicin.
TUC Za Ta Hada Kai Da PENGASSAN Wajen Shiga Yajin Aiki Saboda Matakin Matatar Dangote
