Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce Najeriya na daga cikin kasashen Afrika da ke da mafi yawan mace-mace sanadiyyar hatsarin mota, inda ake samun mutuwa 21.4 a cikin kowace 100,000 na jama’a.
Justice Monica Dongban Mensem, shugabar ƙungiyar Kwapda’as Road Safety Demand (KRSD), ta ce wannan adadi ba wai lissafi ba ne kawai, “amma yana nuna dubban iyalai na shiga cikin tashin hankali duk shekara.”
Shugaban FRSC, Shehu Mohammed, ya tabbatar da cewa hukumar za ta ƙara ƙaimi wajen rage hatsura, tare da kafa cibiyoyin agajin gaggawa ga waɗanda suka jikkata.
Wani direba mai gogewa, Pius Akwashiki, ya bayyana dalilan manyan hadurra a Najeriya da suka haɗa da: mugayen hanyoyi, lalatattun motoci, da kuma halayen direbobi. Ya ba da shawarar gwamnati ta gyara hanyoyi, ta tsaurara binciken lafiyar motoci, tare da hana direbobi marasa kwarewa ci gaba da aiki.
WHO Ta Bayyana Tsananin Yawaitar Hadurran Mota A Najeriya
