Kotun Sojoji ta musamman da ke zama a sansanin Maxwell Khobe, Jos, ta yanke wa wani soja mai suna Private Lukman Musa hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe wani mai keke napep, Abdulrahman Isa, a garin Azare na jihar Bauchi.
Kotun, wacce shugaban ta ne Brigadier Janar Liafis Bello, ta tabbatar da Musa da laifin kisan kai, mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, da kuma kisan kai mai laifi (culpable homicide).
Binciken kotu ya gano cewa Musa tare da wani abokin harkallarsa mai suna Oba, sun yaudari marigayin Isa da zancen taimakawa wajen kwashe kaya. Daga baya Musa ya doke shi da katako sannan ya shake shi har lahira.
Don ɓoye laifin, an tabbatar da cewa Musa ya saka gawar cikin jaka ya jefar da ita a tsakanin kauyukan Shira da Yala, sannan daga baya aka sayar da kekensa. Haka kuma an kama shi da harsasai guda 34 na 7.62mm ba tare da izini ba.
Kotun ta yanke masa hukuncin kisa bisa sashin 220 na kundin Penal Code, wanda ya tanadi hukunci a karkashin sashin 221. Haka kuma an yanke masa shekaru biyu a gidan yari saboda mallakar makamai ba bisa ka’ida ba tare da kora daga rundunar sojin Najeriya da tozarci.
Mai ba da shawara na 3 Division Legal Services, Major Aminu Mairuwa, ya ce hukuncin ya nuna cewa rundunar sojojin Najeriya ba za ta lamunci rashin bin doka ba.
Soja Zai Sha Hukuncin Kisa A Jos Bisa Laifin Kashe Wani Matuƙin Keke Napep
