Mutane biyu sun rasa rayukansu a wani mummunan hatsari da ya afku a kauyen Pasa, kan titin Ilorin–Jebba, a Karamar Hukumar Moro ta Jihar Kwara, ranar Talata.
Wadanda suka mutu a lamarin su ne direban tankar da kuma yaron motarsa.
Rahotanni sun ce hatsarin ya faru ne da misalin karfe 3:43 na rana lokacin da wata tanka mai dauke da lita 30,000 na man fetur, mai lamba NSR 966 ZQ, ta yi taho-mu-gama da hanya, ta kife sannan ta kama da wuta.
Jami’in hulda da jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara, Hassan Adekunle, ya bayyana cewa: “Emergency crews arrived promptly and extinguished the blaze, preventing further spread to nearby traffic. Sadly, the driver and the motor boy lost their lives immediately at the scene of the accident.”
Daraktan hukumar, Prince Falade John Olumuyiwa, ya yi ta’aziyya ga iyalan mamatan tare da yin kira ga direbobi da sauran masu amfani da hanya da su kasance cikin taka-tsantsan a hanya.
Ya kuma jaddada bukatar yin gyaran mota akai-akai, kiyaye ka’idojin saurin tuki, guje wa yin tafiye-tafiye da dare idan babu dalili mai karfi, da kuma samun isasshen hutu domin kauce wa gajiya a lokacin tuki.
Haka kuma, ya shawarci direbobi da sauran masu ababen hawa da su rika dauke da kayan kashe wuta a cikin motocinsu tare da sanar da hukumar kashe gobara cikin gaggawa idan wani lamari ya faru, domin samun dauki cikin lokaci.
Hatsarin Tankar Mai Ya Halaka Mutane Biyu a Jihar Kwara
