Rahotanni sun bayyana cewa wasu ’yan bindiga sun halaka wani jami’in Hukumar Kwastam a kan iyakar shingen bincike na Fingila, a Karamar Hukumar Dandi ta Jihar Kebbi, a ranar Litinin.
Wani mazaunin kauyen Fingila mai suna Malam Abdulrasheed ya ce kafin kai harin, maharan sun shiga gonaki inda suka tsoratar da manoma.
A cewar sa, “Sun shiga gonakin suka tilasta wa manoman su dandana abincin da suka kawo daga gida. Bayan haka sai su ma ’yan bindigan suka ci ragowar abincin sannan suka ce wa manoman su tashi, babu noma a yau.”
Ya bayyana cewa maharan, kimanin su bakwai dauke da manyan makamai a kan babura, daga bisani suka nufi babban hanya inda suka tarar da jami’in Kwastam yana zaune a bakin wani masallaci, suka bude masa wuta.
“Ko da harbin farko bai same shi ba, sai na biyu ya riske shi lokacin da yake kokarin tserewa zuwa gonar masara. Sai na uku ya kashe shi a cikin gonar,” in ji Abdulrasheed.
Rahotanni sun kara da cewa wasu jami’ai biyu na Kwastam da ba su fito fili ba lokacin harin sun tsira ta hanyar rarrafe a cikin gonar masara, kodayake sun samu raunuka kadan.
Mutumin da aka kashe an ce asalin sa daga Maiduguri ne a Jihar Borno, kuma ana yawan ganinsa yana zama kusa da masallacin da aka harbe shi.
’Yan Bindiga Sun Hallaka Jami’in Kwastam a Jihar Kebbi
