Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Haruna Aliyu Dangyatin, ya sha da kyar bayan hadarin da ya rutsa da jerin motocin rakiyarsa a hanyarsa ta zuwa Maigatari.
Dangyatin yana kan tafiya zuwa wani gangamin siyasa na gwamnati mai taken “Gwamnati da Jama’a” lokacin da hadarin ya auku.
Rahotanni sun bayyana cewa daya daga cikin motocin rakiya, Toyota Hilux mai dauke da jami’an ‘yan sanda, ta kauce daga hanya ta kuma yi ta-giya, abin da ya jefa jami’an da ke ciki waje.
Wani ganau ya ce motar Kakakin da sauran motocin rakiyar sun tsaya da kyar, ba fiye da ‘yan mitoci daga wurin da hatsarin ya faru ba.
Jami’an da suka jikkata an garzaya da su Asibitin Gwamnati na Gumel, inda aka ce sun shiga cikin rashin hayyaci, amma daga bisani likitoci suka farfado da su.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Mataimakin Shugaban Majalisa na Musamman, Aqeel Akilu, ya bayyana cewa babu wanda ya rasa ransa, kuma dukkan ‘yan sandan da abin ya rutsa da su sun warke.
Kakakin Majalisar Dokokin Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya
