Rundunar ’yan sandan jihar Adamawa ta ce ta samu nasarar kubutar da wasu yara biyar da ake zargin an sace su daga Maiduguri a jihar Borno, aka kawo su Mubi da ke jihar Adamawa.
Mai magana da yawun rundunar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, cikin wata sanarwa ya bayyana cewa, a ranar 13 ga Satumba, 2025, Kwamandan yankin Mubi, ACP Marcos Mancha, ya jagoranci tawagar sintiri bayan samun sahihan bayanai, inda suka gano yaran suna yawo ba tare da sanin inda za su ba a titunan garin Mubi.
Sanarwar ta ce yaran da aka kubutar sun haɗa da:
Adamu Musa (16),
Suleiman Idris (10),
Suleiman Mohammed (11),
Dauda Yahaya (11),
Mohammed Alhassan (11).
Dukkansu mazauna unguwar Gwange ne da ke Maiduguri a jihar Borno.
Binciken farko ya nuna cewa wani mutum mai suna Aliga Suleiman daga Sabon Layi, unguwar Gwange a Maiduguri, shi ne ya ɗauke su ba bisa ka’ida ba, kuma a yanzu ya tsere.
Rundunar ta bayyana cewa tana ci gaba da kokarin cafke wanda ake zargin domin gurfanar da shi a gaban shari’a.
’Yan Sanda Sun Ceto Yara Biyar da Aka Sace a Jihar Adamawa
