Wani manomi mai suna Mr. Tachia Akor ya rasa ransa bayan wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari a garin Tse Akor Gbatse, da ke cikin Mbamar, yankin Nyiev, a karamar hukumar Guma ta jihar Benue, a daren Lahadi.
Maharan sun kai harin ne tsakanin ƙarfe 12 zuwa 1 na dare, inda suka harbe Akor har lahira, sannan suka jikkata matarsa da kuma wata mata mai suna Mrs. Mbagbedi Tsetim. An garzaya da su asibitin Adi da ke garin Daudu domin samun kulawa.
Rahotanni daga mazauna yankin sun ce wasu mutane sun nemi mafaka a lokacin harin, lamarin da ya haifar da tsoro a cikin al’umma.
Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa wannan hari ya biyo bayan gargadin da suka bai wa gwamnatin jihar Benue da hukumomin tsaro cikin sa’o’i 24 da suka gabata, game da yiwuwar farmaki daga wasu da ake zargin yan bindiga ne.
An ce tun ranar 12 ga watan Satumba, an samu bayanan leƙen asiri da ke nuna cewa wasu ’yan bindiga da ke zaune a Rukubi, karamar hukumar Doma a jihar Nasarawa, na shirin kai farmaki a iyakokin Guma. Rahoton ya nuna cewa sun zargi mutanen yankin da hannu a bacewar ’ya’yansu guda uku mako guda da ya gabata.
A lokacin harin, maharan sun harbe Mr. Akor har ya mutu, inda daga bisani aka kai gawarsa dakin ajiye gawa na asibitin Daudu. Mazauna yankin sun ce maharan har yanzu ana ganin su suna yawo a kauyukan inda suka roki gwamnati ta dauki matakin gaggawa wajen fatattakar su.
Da yake tabbatar da lamarin, kakakin rundunar ’yan sanda na jihar Benue, DSP Udeme Edet, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun riga sun isa yankin domin dawo da zaman lafiya.
Mahara Sun Hallaka Manomi, Sun Jikkata Mutane Biyu a Jihar Benue
