Dakarun tsaro sun tabbatar da dawowar zaman lafiya a kauyen Dadu da ke karamar hukumar Kwali a Babban Birnin Tarayya, bayan tashin hankalin da ya faru tsakanin manoma da makiyaya a ranar Juma’a.
Rahoton Zagazola Makama ya nuna cewa rikicin ya barke ne bayan shanu sun shiga gona mallakar wani manomi mai suna Yunana Garba. A yayin arangamar, ɗansa Yunana Naroka ya samu rauni a kai sakamakon sara da adda, yayin da shi kansa Garba aka bugi wuyansa da sanda na kiwo.
Wata mata ’yar Fulani mai suna Amina Abdullahi ta kuma samu rauni a tafin hannunta saboda sara da adda a lokacin rikicin.
An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Goje Clinic da ke Ijah, da kuma Abu Fatima Hospital a Kwali. Likitoci sun tabbatar da cewa suna samun sauƙi.
Bayan faruwar lamarin, tawagar haɗin gwiwa ta sojoji, ’yan sanda, jami’an DSS da kuma ’yan sa kai sun isa yankin domin kwantar da tarzomar.
Hukumomi sun ce an dawo da zaman lafiya, sai dai bincike kan abin da ya faru yana ci gaba.
An Yi Nasarar Kwantar Da Rikici Tsakanin Manoma Da Makiyaya A Abuja
