Sojojin Runduna ta 1 sun cafke wata mata da ake zargin tana taimaka wa ‘yan ta’adda a garin Kanoma da ke jihar Zamfara.
Matar, mai suna Fatima Isah Ile, an kama ta ne a cikin wani ginin da bai kammala ba a wajen garin, inda ake zargin tana amfani da yara wajen sayen man fetur.
Majiyoyin tsaro sun shaida wa Zagazola Makama cewa bincike ya nuna matar ita ce matar sanannen dan ta’adda, Isah Ile. A yayin wannan samame, sojoji sun gano jarkoki uku na man fetur.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an mika wadda ake zargin ga Hukumar Tsaro ta DSS domin gudanar da cikakken bincike.
Sojoji Sun Kama Wata Da Ake Zargi Matar Shahararren Dan Ta’adda Ne A Zamfara
