Kamfanin Dangote Refinery ya sanar da rage farashin litar man fetur a fadin Najeriya, tare da bayyana cewa zai fara sabon shirin rarraba mai kai tsaye daga ranar Litinin, 15 ga Satumba, 2025.
Shirin, wanda aka tsara tun farko a fara shi ranar 15 ga Agusta, 2025, zai bai wa kamfanin damar rarraba man fetur da dizal kai tsaye ta manyan motocinsa 4,000 masu amfani da iskar gas (CNG), ba tare da ƙarin kuɗin jigila ba.
Dangote Refinery, wadda take da karfin tace ganga dubu 650 a rana, ta ce sabon farashin lita a gangaranta zai ci gaba da kasancewa N820, kamar yadda ta sanar a watan da ya gabata.
A cewar sabon tsarin farashin da aka wallafa a shafin kamfanin na X, a jihohin Legas, Oyo, Ogun, Ondo da Ekiti, farashin lita zai kasance N841 maimakon N860.
A Abuja, Edo, Delta, Rivers da Kwara kuwa, farashin zai sauka daga N885 zuwa N851 a kowace lita. Wannan na nufin raguwar N19 a farashin lita a yankin Kudu maso Yamma, da kuma N34 a Abuja, Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Kudu.
Kamfanin ya bayyana cewa wannan sabon tsarin farashin da kuma shirin rarraba kai tsaye zai fara aiki ranar Litinin mai zuwa, 15 ga Satumba, 2025.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa tsarin farashin da Dangote ta fitar ba ya daure sauran dillalan mai da ‘yan kasuwa, banda kamfanin MRS da sauran abokan harkarsa.
A gefe guda, ƙungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas (NUPENG) ta yi barazanar komawa yajin aiki kan Dangote Group, tana zargin kamfanin da karya yarjejeniyar da aka cimma kwanan nan.
Amma kamfanin Dangote ya ce yana mutunta ‘yancin ma’aikatansa na yin rajista da ƙungiya ko kuma akasin haka.
Matatar Dangote Ta Rage Farashin Man Fetur a Fadin Najeriya
