Ƴan Sanda Sun Kama Ɓarayin Daji 46 a Jihar Kwara

Rundunar ƴan sandan Jihar Kwara ta bayyana cewa jami’anta sun cafke mutane 46 da ake zargi da kasancewa cikin Ƙungiyar Ɓarayin Daji, a wani samame da aka gudanar a yankin Babanla, ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar.

Wata majiya ta tsaro ta bayyana cewa an yi nasarar cafke mutanen ne bayan makonni na sa ido a yankunan da aka dade ana fuskantar hare-haren daji da kuma satar mutane. Rahotanni sun nuna cewa an kama su ne a kan babura, daga bisani aka kaisu Ilorin, babban birnin jihar, cikin wata babbar mota ta Coaster a karkashin tsauraran matakan tsaro.

Al’ummar Babanla ta fuskanci hare-hare da dama a kwanakin baya wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane tare da sace wasu. Wannan ya janyo tsoro da kuma jita-jita a shafukan sada zumunta, inda wasu ke zargin cewa manyan mutane na da hannu a cikin lamarin.

Da yake karin bayani ga manema labarai, Kwamishinan ƴan sandan jihar, Adekimi Ojo, ya karyata rade-radin da ke cewa an kama Sarkin Babanla, Oba Aliyu Adegboyega Yusuf, Arojojoye II, tare da matansa.

Wata jarida a kafafen sada zumunta ta yada cewa an kama Sarkin ne bayan gano naira miliyan 120 daga kudaden Ɓarayin Daji, inda aka ce an samo naira miliyan 90 daga fadarsa da kuma miliyan 30 daga asusun bankin matarsa.

More from this stream

Recomended