Zai tafi hutun kwanaki 10 a kasashen Faransa da Birtaniya 

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai tafi Nahiyar Turai a ranar Alhamis inda zai yi hutun kwanaki 10.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Onanuga ya ce Tinubu zai shafe kwanaki 10 na hutunsa na shekara a kasashen Faransa da Birtaniya kafin daga bisani ya dawo gida Najeriya.

Tun bayan da aka rantsar da shi a shekarar 2023 shugaban kasar ya shafe sama da kwanaki 200  a kasashen waje inda yake shan suka daga yan adawa dama wasu al’ummar Æ™asar.

More from this stream

Recomended