
An naɗa, Alhaji Sanusi Mika’il Sami Gomo a matsayin sabon Sarkin Masarautar Zuru.
Kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu na jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Garba Dutsin-Mari ne ya sanar da nadin a ranar Alhamis a fadar Masarautar Zuru lokacin da yake mikawa sabon sarkin takardar nadin dake ɗauke da sahannun gwamnan jihar Nasir Idris.
Ya ce an naɗa Sarkin ne bayan da masu zaɓen sarki na masarautar suka mikawa gwamnan sunayen mutane uku kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Ya kara da cewa gwamnan ya yi amfani ikon da doka ta bashi inda ya nada, Alhaji Sanusi Mika’il Sami a matsayin sabon Sarkin Zuru da za a rika kiransa da suna Gomo III.
Tun da farko, Sarkin Wasagu, Alhaji Muktari Musa wanda ya rike muƙamin sarkin masarautar na riko tun bayan rasuwar marigayin ya karbi sabon sarkin a hukumance tare da yin marhabun ga dukkanin bakin da suka halarci fadar.
A jawabinsa sabon sarkin ya mika godiyarsa ga Allah da kuma gwamnan jihar Kebbi kan aminta da suka yi da shi.