
Rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta kama wani da ake zargin gawurtaccen mai garkuwa da mutane ne a maboyarsa dake wani daji a ƙaramar hukumar Soma ta jihar.
A wata sanarwa ranar Lahadi mai magana da yawun rundunar, Ramhan Nansel ya ce “gawurtaccen dan fashi kuma mai garkuwa da mutane,” ya fada hannun yan sandan dake aiki a ofishin yan sanda na Doma.
Nansel ya ce farmakin da ya kai ga kama shi wani bangare ne na kokarin da rundunar take baji ba gani na yaki da bata gari a jihar.
Ya ce wanda aka kama ya fito ne daga kauyen Yelwa dake yankin shi ne yake da alhakin aikata jerin fashi da makami da kuma garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Doma da kewaye.
“Wanda ake zargin ya tsallake rijiya da baya a watan Yulin shekarar 2023 lokacin da aka kama mutanensa,” a cewar sanarwar.
Sanarwar ta ce jami’an tsaro ne suka kama shi a dajin Doka.