
Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince a kashe naira biliyan ₦142.02 domin a gina sababbin tashoshin mota na zamani a shiyoyi guda shida da ake da su a ƙasarnan.
Sa’idu Alkali ministan sufuri shi ne ya sanar da haka lokacin da yake yiwa yan jaridu jawabi a ranar Laraba bayan zaman majalisar zartarwa ta tarayya a fadar Aso Rock dake Abuja da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya jagoranta.
Alkali ya ce an bada kwangilar gina tashoshin ga kamfanin Planet Project Limited a garuruwan Abeokuta (yankin kudu maso yamma), Gombe (arewa maso gabas), Kano (arewa maso yamma), Lokoja (arewa ta tsakiya), Onitsha (kudu maso gabas), da kuma garin Ewu dake jihar Edo a yankin kudu maso kudu.
Ministan ya bayyana samar da tashoshin a matsayin zuba jari irinsa na farko da gwamnatin tarayya ta yi wajen samar da abubuwan more rayuwa a fannin sufuri bayan gina tituna.
Alkali ya ce ma’aikatar ce ta tsara samar da tashoshin kuma ta samu sahalewar majalisar zartarwar bayan da ta yi duba na tsanaki kan shirin.