
Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Uba SaniĀ ya cire Muhammad Bello daga mukaminsa na kwamishinan yada labarai na jihar inda ya nada Ahmad Maiyaki a madadinsa.
A wata sanarwa da aka fitar ranar Talata, Ibrahim Musa mai magana da yawun gwamnan ya ce nadin da aka yi wa Maiyaki ya fara aiki ne nan take ba tare da bata lokaci ba.
Kafin nadin nasa, Maiyaki ya kasance shugaban hukumar kula da kafafen yada labarai ta jihar Kaduna kafin a nada shi mukamin kwamishina.
A yayin da ba a bada wani dalili ba na cire Bello mai magana da yawun gwamnan ya ce kafin a nada shi kwamishinan yada labarai, Bello ya kasance kwamishinan a ma’aikatar ilimi.
Ya kara da cewa gwamnan ya mika godiyarsa tga Bello kan ayyukan da ya yi tare da yi masa fatan nasara a rayuwarsaĀ ta nan gaba.
Amma kuma a ranar Talata ne Bello ya fitar da takardar yin murabus dan kashin kansa daga kwamishina kuma mamba a majalisar zartarwa ta jihar.