‘Yan Bindiga Sun Lalata Gona a Katsina, Sun Kai Hari Wurma Amma Jami’an Tsaro Sun Mayar da Martani

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun lalata gonaki a kauyen Dungun Mu’azu da ke karamar hukumar Sabuwa a Jihar Katsina.

Wani masani kan harkar tsaro mai suna Bakatsine ne ya bayyana hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X (tsohon Twitter) a ranar Juma’a.

A cewarsa: “Mazauna Dungun Mu’azu da ke karamar hukumar Sabuwa a Jihar Katsina sun wayi gari da gonakinsu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka lalata. Wannan lamari mai tayar da hankali idan ba a shawo kansa ba, ka iya jefa ƙasar cikin matsanancin ƙarancin abinci nan da watan Disamba.”

A wani lamari da ya faru a ranar Juma’a da rana, wasu ‘yan bindiga sun yi ƙoƙarin kai hari a garin Wurma da ke karamar hukumar Kurfi ta jihar Katsina, amma sun gamu da ƙawanya daga jami’an Community Watch Corps (CWC) da kuma masu gadin gari.

A cewar Bakatsine: “Da rana, ‘yan bindiga sun ƙuduri aniyar kai hari a garin Wurma da ke Kurfi a Katsina, amma suka gamu da tsayayyen martani daga CWC da vigilante. Ko da yake ‘yan bindigar sun fi su ƙarfin makami, ba su yarda sun shige garin ba. Abin bakin ciki, wasu daga cikin jami’an tsaron sun jikkata.”

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, hukumomi ba su fitar da wata sanarwa kan harin ba.

More from this stream

Recomended