

Shugaban majalisar dattawa, sanata Godswill Akpabio ya shigar da kara a gaban kotun daukaka kara dake Abuja inda yake kalubalantar umarnin da kotu ta bayar na janye dakatarwar da majalisar dattawa ta yiwa sanata, Natasha Akpoti Uduaghan.
A ranar 4 ga watan Yuli ne babbar kotun tarayya dake Abuja ta bayar da umarnin janye dakatarwar da aka yiwa, Natasha Akpoti saboda dakatarwar da aka yi mata na watanni shida ya yi tsauri har ila yau kotun ta ci Natasha tarar naira miliyan biyar kan saba umarnin da kotun ta bayar na kowane bangare a shariar ya kama bakinsa kan batun har sai ta yanke hukuncin.
A daukaka karar da lauyoyinsa suka yi a gaban kotun, Akpabio na rokon kotun da ta jingine hukuncin da aka yi inda ya ce kotun ta yi kuskure da ta yarda cewa tana da hurumim sauraron karar.
Akpabio ya ce batun magana ce ta cikin gida da ya shafi majalisar kuma baya bukatar tsoma bakin bangaren shari’a kamar yadda sashe na 251 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 ya bayyana.