Yobe: Gwamna Buni Ya Umurci Shugabannin Kananan Hukumomi Da Sarakunan Gargajiya Su Fara Yaki Da Sha Da Fataucin Miyagun Kwayoyi

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya umarci shugabannin kananan hukumomi guda 17 da ke jihar tare da hadin gwiwar sarakunan gargajiya da su dauki matakai cikin gaggawa domin dakile yaduwar shaye-shaye da fataucin miyagun kwayoyi a fadin jihar.

Gwamna Buni ya bayyana haka ne a garin Damaturu, yayin wata ganawa da shugabannin kananan hukumomi da sarakunan gargajiya da aka shirya domin duba hanyoyin inganta fannin kiwon lafiya na matakin farko a jihar.

A cewarsa: “Dole ne mu dauki matakin gaggawa tun da wuri domin ceton matasanmu da makomar jiharmu daga barazanar da shan miyagun kwayoyi ke haifarwa, wanda ke kara kamari a wasu jihohin arewacin kasar nan.”

Gwamnan ya kuma jaddada cewa dole ne a tabbatar doka ta yi aiki kan duk wanda aka kama da laifin safarar ko shan kwayoyi da aka haramta a jihar.

Gwamna Buni ya yaba da irin goyon bayan da gwamnatin tarayya, kungiyoyin ci gaba da kuma sarakunan gargajiya ke bayarwa wajen inganta harkar kiwon lafiya a jihar.

Ya ce: “Gwamnatin nan tana da cikakken kuduri wajen tabbatar da isasshen kulawar lafiya a kowane mataki saboda lafiyar jama’a muhimmin jari ne ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma.”

Ya kara da cewa: “Mun kafa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda 142 da ke aiki yadda ya kamata tare da samar da kayayyaki, magunguna da kuma daukar ma’aikatan lafiya fiye da 2,000 wadanda aka tura zuwa cibiyoyi daban-daban a fadin jihar. Wannan kokari ya daga darajar fannin kiwon lafiya a jihar Yobe matuka.”

More from this stream

Recomended