
Matatar mai ta Dangote ta kara farashin kudin man fetur da take samarwa ya zuwa naira N880 kan kowace lita.
Karin ya kama N55 ne kan kowace lita idan aka kwatanta da farashin da ake sayar da man a baya na N825 kan kowace lita.
Abubakar Shettima shugaban kungiyar dillalan man fetur ta IPMANĀ ya tabbatar wa da jaridar The Cable karin a zantawar da ya yi da su a ranar Lahadi.
“Muna sane da cewa matatar man ta sauya farashin man fetur ya zuwa N820 kowace lita.An sanar da mambobin mu, ” ya ce.
Karin na zuwa ne dai-dai lokacin da matatar ta sanar da sayen motoci dakon mai domin fara kai wa kwastomominsu ko ina a fadin Najeriya.