


Mataimakin shugaban kasa,Kashim Shettima ya sanar da cewa gwamnatin tarayya ta bayar da tallafin naira biliyan biyu ga al’ummar da ambaliyar ruwa ta yiwa mummunar barna a garin Mokwa hedkwatar karamar hukumar Mokwa ta jihar Neja.
Shettima ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido garin domin jajantawa al’ummar da abun ya shafa.
Ya kara da cewa gwamnatin tarayya tayi alkawarin samarwa da mutanen tallafin gaggawa.
” A yau na ziyarci al’ummar da ambaliyar ruwa ta shafa inda gwamnatin tarayya ta bayar da tallafin naira biliyan 2 da kuma motoci 20 na hatsi ga mutanen da abun ya shafa,”a cewar Shettima cikin wani sako da ya wallafa a Facebook.
A yayin ziyarar Shettima na tare da ministan yada labarai, Mohammed Idris Malagi