Yan sanda sun  kama wasu dillalan kwayoyi a jihar Anambra

Rundunar yan sandan jihar Anambra ta kama wasu mutane 6 da ake zargi da aikata safara da kuma rarraba miyagun kwayoyi.

A wata sanarwa ranar Asabar Mai dauke da sahannun, Tochukwu Ikenga mai magana da yawun rundunar ya ce an kama mutanen ranar Juma’a a garin Isuaniocha dake karamar hukumar Awka north ta jihar.

Wadanda aka kama sun hada da Chinyere Onwuka, shekaru 32 ; John Kennedy Onwuka, shekaru 36 ; Chidiebere Onyeze, shekaru 30 ; Echeazu Nonso, shekaru 35 ; Osita Chukwu Chialuka, shekaru 21 ; da kuma Nnebedum Wisdom, shekaru 25.

Ikenga an samu wani kaso mai yawa na busasshen ganye da ake zargin kwaya ce da kuma abubuwa da dama na laifi.

Ya ce za a mika dukkanin mutanen ga hukumar NDLEA dake yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi domin zurfafa bincike da gurfanar da su a gaban kotu.

Ya kara da cewa kwamishinan yan sandan jihar ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake samun karuwar ta’ammali da miyagun kwayoyi a tsakanin matasa inda ya ce kwaya ita ce silar aikata laifuka da dama da kuma haifar da wasu dabi’u marasa kyau.

More from this stream

Recomended