Ƴan sanda sun sake cafke wani ɗan fursuna da ya tsere daga gidan gyaran hali na Ilesa

Rundunar ’yan sandan jihar Legas ta sake kama wani ɗan fursuna mai suna Kabiru Oyedun, wanda ya tsere daga gidan gyaran hali na Ilesa da ke jihar Osun.

Oyedun, ɗan shekara 39, na daga cikin fursunonin da suka tsere ne ta wani ɓangare na katangar gidan yari da aka ce ya sami lahani. An cafke shi ne a unguwar Ayobo da ke jihar Legas da misalin ƙarfe 5:30 na yamma a ranar Talata, 21 ga watan Mayu, 2025.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa kama Oyedun ya biyo bayan cikakken sa ido da amfani da dabarun leƙen asiri da rundunar ta yi.

Rahotanni daga rundunar sun nuna cewa an shirya mika Oyedun ga hukumar kula da gidan gyaran hali domin a mayar da shi jihar Osun.

Tun a baya dai Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS) ta sanar da fara farautar waɗanda suka tsere daga gidan yari na tsaka-tsaki da ke Ilesa, wanda aka ce ruwan sama mai ƙarfi ne ya jawo rugujewar wani ɓangare na katangarsa.

More from this stream

Recomended